Taron zai hada Shuwagabannin kasashen Najeriyar da Nijar da Kamaru da Benin da kuma na Chadi domin duba hanyar da za a bi domin kawar da kungiyar Boko Haram.
Wakilan Amurka da na kungiyar Gamayyar Turai da kuma na Birtania, su ma za su shiga taron.
Tattaunawar dai za ta yi nazari a aikin da kwararrun da Birtania da Faransa da Amurka suka tura Najeriyar domin su taimaka a gano 'yan matan nan na Chibok da 'yan Boko Haram suka sace. ABNA.